1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Weah ya sha kaye a zaben shugaban kasar Laberiya

Mouhamadou Awal Balarabe
November 18, 2023

Jami’an zaben Laberiya sun tantance 99.58% na kuri’un da aka kada, inda Joseph Boakai ke kan gaba da 50.89% yayin da George Weah ya samu 49.11%. Weah ya ja hankalin mabiyansa da su amince da sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/4Z7qW
George Manneh Weah ya sha kaye bayan wa#adi daya na mulki a Laberiya
George Manneh Weah ya sha kaye bayan wa#adi daya na mulki a LaberiyaHoto: Peter Dejong/AP/picture alliance

Shugaban kasar Laberiya George Weah ya amince da shan kaye a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a ranar Talata, bayan da sakamakon farko ya nuna cewa abokin hamayyarsa Joseph Boakai ne ke kan gaba da mafi rinjayen kuri'un da aka kada. Jami'an zaben na kasar sun riga sun tantance 99.58% na kuri'un, inda Boakai ke kan gaba da 50.89% yayin da Weah ya samu kashi 49.11%.  Idan za a iya tunawa dai, da irin wannan sakamakon ne George Weah ya doke Joseph Boakai a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Laberiya da ya gudana shekaru shida da suka gabata.

A jawabin da ya yi wa al'ummar kasarsa, Shugaba Weah ya ce zai mutunta zabin masu kada kuri'a, amma zai sake tsayawa takara a shekara ta 2029. Sannan ya ja hankalin mabiyansa da su yi koyi da shi wajen amincewa da sakamakon zaben. Weah ya yi wannan jawabin ne tun ma kafin a bayyana sakamakon a hukumance a Laberiya, a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan tabarbarewar dimokuradiyya a kasashen yammacin Afirka.