1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kotu a ƙasar Masar ta yanke hukumci akan takarar 'zaɓe

November 14, 2011

Za a dama da tsofin manbobin jam'iyar PND ta tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak a zaɓɓuɓukan yan majalisun dokin da za a gudanar a ƙarshen wannan wata

https://p.dw.com/p/13AV9
Hosni Mubarak tsohon shugaban ƙasar MasarHoto: dapd

Wata kotun kolli a ƙasar Masar ta yanke hukumcin bayar da izini ga tsofin menbobin gwamnatin mulkin kama karya ta Hosni Moubarak;domin tsayawa takara a zaɓen yan majalisun dokokin da aka shirya gudanarwa a ƙarshen wannan wata.

A ranar juma'a da ta gabata ne wata kotun ta garin Mansoura da ke akan kogin Nilo ta haramta wa tsOfin mAnbobin jam'iyar ta PND tsayawa takara kafin da ga bisanin babbar kotun kollin ta karya hukumcin;wannan zaɓɓUuɓuka da za a gudanar za su bada damar girka sabuwar majalisar dokoki wacce zata kafa wani kwamitin da zai rubuta kundin tsarin mulki na ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal