1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko ta yankewa 'yan IS hukuncin kisa

Ramatu Garba Baba
July 18, 2019

Kotu ta yanke wa wasu mayakan IS 3 hukuncin kisa bayan da aka same su da laifin hannu a fille kawunan wasu Turawa, masu yawon bude ido a kasar a Disambar bara.

https://p.dw.com/p/3MHWD
Marocco | Prozess, Mord Skandinavischer Frauen
Hoto: AFP/Getty Images/F. Senna

An kwashi sama da watanni uku ana shari'ar Abdessamad Ejjoud, wanda shi ya jagoranci fille kawunan matan da suka fito daga kasashen yankin Scandinavia. Masu shigar da kara sun dage kan a zartas da hukuncin kisan, duk da cewa, Moroko ta soke amfani da dokar tun shekarar 1993. 

Matan biyu 'yan shekaru ashirin da hudu, sun gamu da ajalinsu ne a yayin wata ziyara da suka kai kasar ta Moroko a Disambar bara. Kungiyar IS dai ba ta fito fili ta amince da hannu a kisan ba sai dai wadannan da suka ce su 'yan kungiyar ne sun amsa laifukan kisan matan.