Wata Kotu a Masar ta yanke hukunci a kan wasu ' yan ƙasashen waje.
June 4, 2013Talla
Wata kotu a birnin Alƙahira na ƙasar Masar ta zartar da hukuncin ɗaurin shekaru ɗaya zuwa biyar ga wasu gungun wakilai na ƙungiyoyin masu zaman kansu 43 waɗanda ta ke tuhuma da gudanar da ayyuka ba bisa ƙaida ba, ta hanyar samar da kuɗaɗen haram. Daga cikin mutanen guda 43 da aka yanke wa hukunci, 27 an yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru biyar kana wasu 16 aka yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru biyu ciki har da wani Ba'amirke.
An gabatar da mutanen ne a gaban Kotun, tun a shekara ta 2012 bayan binciken da aka gudanar a kan ƙungiyoyin da suke jagoranta waɗanda suka haɗa da Konrad Adenauer ta Jamus da NDI National democratic Institue ta Amirka.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh