1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata cuta ta bulla a Kwango

March 7, 2021

Kimanin shekaru sama da dari ba a ga makamanciyar irin wannan cutar ba a Kwango, cutar ta sake bulla a kasar.

https://p.dw.com/p/3qKRs
Beulenpest
Hoto: Gemeinfrei

Baya ga cutar coronavirus da ta Ebola da suka addabi al'umma a Kwango, wata sabuwar cutar da ba a tatntanceta ba ta bulla a kasar.

An dai taba samun makamanciyar irin wannan cutar a iyakokin kasar ta Kwango da Yuganda da kuma Sudan ta Kudu a yanzu kimanin shekaru kusan dari da suka wuce.

Ana daukar cutar ne daga Kuma da bakaken Beraye ya zuwa ga bil adama, cutar kan bulla lokaci zuwa lokaci amma daga bara ne abin ya fara yin kamari.

Kawo yanzu babu alkaluman wadanda suka rasu ko kamuwa da ita.