1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu muƙƙarraban shugaban Siriya sun juya masa baya

April 28, 2011

Kimanin membobin 200 na jam'iyar Baath ta Bashar Al-Assad na Siriya sun nesanta kansu da kashe-kashen fararen hula 450 da ake zargin shugaban da aikawata.

https://p.dw.com/p/115S5
Shugaba Bashar al-Assad na SiriyaHoto: dpa

Wasu ƙusoshin jam'iyar da ke jan ragamar mulkin Siriya sun yi murabus daga muƙamansu, da nufin nuna rashin jin daɗinsu da amfani da ƙarfi fiye da kima da shugaba Bashar Al-assad ke yi domin murƙushe boren ƙin jinin gwamnatinsa. Kimanin mambobi 200 na jam'iyar Baath ne suka fitar da wata sanarwar haɗin guywa domin nesanta kansu da duk wani matakin na tursasawa jama'a da shugaba Al-assad ke ɗauka domin ceto kujerar mulkinsa da ke tangal-tangal.

shugabannin jam'iyun adawa sun nemi Bashar Al-Assad ya hanzarta aiwatar da sauye-sauyen siyasa, ko kuma su matsa ƙaimi domin hamɓarar da shi daga karagar mulki. ƙoƙarin da ƙasashe Turai suka yi domin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da matakin soje da Bashar Al-assad ya ɗauka ya ci tura. sai dai ministan harkokin wajen Jamus, wato Guido Westerwelle ya ce ƙasashen Turai za su yi gaban kansu wajen ƙaƙaba wa Syriya takunkumi.

Wata ƙungiyar ƙasar Syriya da ke da rajin kare hakkin bil Adama ta nunar da cewa mutane 450, sojojin gwamnati suka hallaka tun bayan ɓarkewar zanga-zangar.

Mawallafi Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi