1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu jerin bama-bamai sun fashe a birnin Kano

January 20, 2012

A jihar kano dake arewacin Najeriya an sami aukuwar harin bama-bamai a wasu sassa na birnin.

https://p.dw.com/p/13nSe
***Für mögliche Ergänzungen der Karte, wie z.B. andere Sprachen, zusätzliche Orte oder Markierungskreuz, wenden Sie sich bitte an infografik@dw-world.de (-2566), Außerhalb der Bürozeiten an bilder@dw-world.de (-2555).*** DW-Grafik: Per Sander 2011_03_10_Laender_Prio_A_B
Taswirar ƙasar Tarayyar Najeriya

Rahotanni sun ce an kai harin bama-baman ne a Hedikwatar shiyya ta ɗaya ta 'yan sandan Najeriya dake jihar da ofishin jami'an shige da fice dake Marhaba da kuma wasu ofisoshi biyu na 'yan sanda a unguwannin 'yar Akwa da kuma Unguwa uku. An ruwaito cewa mai yiwuwa hari ne na ƙunar baƙin wake. Wakilin mu a Kano Abdulrahman Kabir yace da misalin karfe biyar na yammacin Juma'ar nan ce aka jiwo ƙarar fashewar bama baman a sassa da dama na birnin na Kano inda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya. Ƙarfin fashewar ya haifar da ruɗani inda masu ababen hawa motoci da babura da kuma masu tafiya a ƙasa kowa ke ta kansa domin tsira da rayuwarsa. Maharan sun kuma kai farmaki Hedikwatar 'yan sanda dake Bompai inda suka yi musayar wuta da 'yan sanda. Ba'a dai tantance girman ta'adin ba tukunna. Bugu da ƙari an kuma kai hari ofishin jami'an leken asiri SSS dake jihar. Ana dai danganta hare-haren bama-bamai dake faruwa a arewacin ƙasar ga ƙungiyar nan ta Ahlul Sunna Lidda'awati wal- jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi