1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga a Tarayyar Jamus

Gazali Abdou Tasawa
December 17, 2018

Borussia Dortmund na ci gaba da yin kane-kane a saman teburin gasar da maki 39,kana takwararta ta Mönchengladbach ke matsayin na biyu da maki 30 bayan da ta tashi banza da banza tsakaninta da Hoffenheim.

https://p.dw.com/p/3AFV3
Fußball Bundesliga Borussia Dortmund - Werder Bremen
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayern Münich wacce ta bi Hannover har gida ta yi mata cin kaca na hudu da babu, na a matsayin ta uku da maki 30 itama.

A sauran wasanni kuma Nuremberg ta sha kashi a gaban Wolfsburg da ci 2-0, ita ma Dusseldorf ta doke Freiburg da ci 2-0, Augsburg da Schalke04 sun tashi daya da daya.

Bugu da kari Leipzig ta lallasa Mayence da ci 4-1, Frankfurt da ta doke Leverkusen da ci 2-1 sai kuma Stuttgart da ta doke Hertha berlin da ci biyu da daya wasan da ya kawo karshe a cikin makoki bayan da jim kadan bayan kammala wasan Allah ya yi wa mahaifin Christian Gentner captain din kungiyar ta Stuttugart rasuwa a filin wasan.