1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin Afirka na share fagen shiga kofin duniya

Lateefa Mustapha Ja'afar Mouhamadou Awal
June 10, 2024

Duk da takun saka da ke tsakanin Hukumar Kwallon Kafar Kamaru da gwamnatin kasar, kungiyar Indomitable Lions ta caskara Cape Verde da ci 4-1 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta 2026.

https://p.dw.com/p/4gsEV
'Yan wasan kwallon kafar kasar Kamaru
'Yan wasan kwallon kafar kasar KamaruHoto: Tnani Badreddine/DeFodi Images/picture alliance

Kamaru ta kwashe kusan shekaru 4 ba tare da zura kwallaye har 4 a raga ba, lamarin da ya jefa 'yan kasar da dama cikin farin ciki bayan da Indomitable Lions ta doke Cape Verde da ci hudu da daya, duk da rigimar da ake samu tsakanin gwamnati da hukumar wasan kwallon kafa. Sai dai da sauran rina a kaba duba da ci gaba da takun saka da ke tsakanin ministan wasanni Narcisse Mouele Kombi da Samuel Eto’o da ke shugabantar hukumar FECAFOOT, wadanda suka kwashe kusan wata guda ba sa ga maciji da juna. Sai dai masu sharhi kan al’amuran siyasa a Kamaru kamar Haruna Ousmanou na cewa rikicin ya samo asali ne daga fadar shugaban kasa.

Ademola Lookman na bada gagarumar gudunmawa a Super Eagles ta Najeriya
Ademola Lookman na bada gagarumar gudunmawa a Super Eagles ta NajeriyaHoto: Weam Mostafa/BackpagePix/empics/picture alliance

Sauran kasashen Afirka sun kece raini a wasanni neman cancantar shiga gasar cin kofin Duniya ta Fifa da za a yi a 2026, inda a rukunin A, Masar ta doke Burkina Faso da ci biyu da daya yayin da Guinea Bissau da Habasha suka yi canjaras babu wanda ya jefa kwallo a raga. A rukunin B, Senegal ta yi kunne doki da Kwango Dimukuradiyya kunnen doki daya da daya yayin da Sudan ta lallasa Mauritania har gida da ci biyu da nema. A rukunin C, Najeriya ta yi kunne doki da Afirka ta kudu kunnen doki daya da daya yayin da Lesoto ta doke Zimbabuwe har gida da ci iyu da nema, ita kuwa Jamhuriyar Benin ta doke Ruwanda da ci daya mai ban haushi.

A rukunin E, Maroko ta doke Zambiya da biyu da daya yayin da aka dage wasa tsaknin Kwango da Jamhuriyar Nijar. A rukunin F, Côte D’ivoire ta yi nasara a kan Gabon da ci daya mai ban haushi, ita kuwa Kenya ta yi kunne doki kunnen doki daya da daya da Burundi. A rukunin G, inda Mozambik ta doke Somaliya da ci biyu da daya, Yuganda kuwa ta yi nasara a kan Botswana da daya mai ban haushi yayin da Aljeriya ta sha kashi a hannun Guniea da ci biyu da daya. Malawi ta baiwa Sao Tome kashi da ci uku da daya a rukunin H. Sai kuma rukunin I inda Ghana ta doke Mali da ci  biyu da daya.

Tasirin zaben Turai wajen shirya olympic a Faransa


A fannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympic da birnin Paris fadar gwamnatin Faransa zai karbi bakunci a lokacin bazara da ke tafe kuwa, shugaban Kwamitin Kula da Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle na Duniya IOC Thomas Bach ya bayyana cewa ya yi imanin bayyana shirin gudanar da sabon zabe a Faransan ba zai shafi gasar ba. Sakamakon zaben Majalsiar Tarayyar Turai da aka gudanar a karshen mako dai, ya nuna yadda jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa ta Marine Le Pen wato National Rally, ta samu gagarumin rinjaye da ya jijjiga jam'iyya mai mulki ta Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.

Thomas Bach, shugaban Kwamitin Olympic na Duniya
Thomas Bach, shugaban Kwamitin Olympic na DuniyaHoto: Laurent Gillieron/dpa/KEYSTONE/picture alliance

Jamus ta shirya caf domin karbar Euro2024


A gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Turai da Jamus ke shirin daukar nauyi, ministan tattalin arzikin Jamus mai masaukin baki Robert Habeck ya ce lokaci ne da kasar za ta murmure bayan shekaru hudu na kalubale. A hirarsa da mujallar wasanni ta Kicker, Habeck ya ce Jamus ta fuskanci kalubalen Corona da kuma matsalar makamashi da tattalin arziki sakamakon yakin Rasha da Ukraine a wadannan shekaru hudun da suka gabata. Koda yake ya nunar da cewa har yanzu akwai matsalar tattalin arzikin a Jamus,amma duk da haka bai kai na shekaru biyun da suka gabata ba kuma gasar za ta taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin kasar da kasa da kaso daya cikin 100. Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda wani bincike na baya-bayan nan da aka yi a Jamus, ya nuna yadda mutum daya cikin biyar da aka ji ra'ayoyinsu ke cewa suna bukatar ganin karin 'yan wasa fararen fata a cikin kungiyar kwallon kafar kasar ta Manscahaft abin da ya bayyana da wani nau'i na wariyar launin fata.

'Yan Jamus na doki da murna game da kofin Turai da kasarsu za ta dauki bakunci
'Yan Jamus na doki da murna game da kofin Turai da kasarsu za ta dauki bakunciHoto: Robin Rudel/picture alliance

Real Madrid ba za ta shiga gasar World Club ba


Mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spaniya Carlo Ancelotti ya ce kungiyarsa da ta lashe kofin zakarun Turai karo na 15 a bana ba za ta shiga gasar kungiyoyin kwallon kafa na kasashen duniya wato Club World Cup da za a fafata a lokacin bazara ba. Ancelotti ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da wata jaridar Italiya, inda ya ce wasan Madrid guda daya kacal ya kai Euron miliyan 20 kuma kudin da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ke son ba su ke nan a baki dayan wasannin da za a yi a gasar. Ya kara da cewa, ya san wasu kungiyoyin wasannin ma za su yi watsi da gayyatar FIFA. Shahararrun 'yan wasan Ingila sun yi gargadi ga hukumar ta FIFA kan wannan gasa da aka kara yawan kungiyoyin da ke halarta zuwa 32 da kuma za a fafata shi a lokacin bazarar bana. 

Verstappen ya kai labari a Formula1

Max Verstappen da Lando Norris da Charles Leclerc bayan samun nasara a Formula 1
Max Verstappen da Lando Norris da Charles Leclerc bayan samun nasara a Formula 1Hoto: Jakub Porzycki/NurPhoto/picture alliance

Shararren dan wasan tseren motocin nan na duniya Max Verstappen ya lashe gasar Canadian Grand Prix a karo na uku a jere ga kungiyarsa ta Red Bull. Wannan dai shi ne karo na 60 da kungiyar tasa ta lashe gasar Formula 1, kana karo na shida a gasar tseren motoci guda tara da aka fafata a kakar wasannin ta bana. Mai shekaru 25 a duniya, dan kasar Neatherlands Verstappen ya kammala tseren tare da lallasa takwaransa dan kasashen Ingila da Beljiyam Lando Norris.