1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Maroko ba ta halartar gasar CHAN

Suleiman Babayo MAB
January 16, 2023

'Yan kwallon Maroko ba su halarci gasar CHAN ba saboda Aljeriya taki amincewa jirgin saman gwamnatin Maroko ya sauka kai tsaye a birnin Algers. An fara daya daga cikin manyan wasannin Tennis na duniya a Ostareliya,

https://p.dw.com/p/4MFlP
'Yan wasan Maroko ba sa halartar CHAN duk da kokari da suka yi a kofin duniyaHoto: KARIM JAAFAR/AFP

Za mu dauko shirin daga Ingila inda a wasan Premier na karon battan gida, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta doke Manchester City da 2 da 1, kana Chelsea ta lallasa Crystal Palace 1 mai ban haushi, sannan Arsenal ta yi tattaki har gida ta doke Tottenham 2 da 0, ita kuma Newcastle ta samu nasara kan Fulham 1 da nema.

Yanzu haka Arsenal ke jagorancin teburin na gasar Ingila da maki, 47, a matsayi na biyu kuwa akwai Manchester City da maki 39, kana a matsayi na uku akwai Newcastle mai maki 38, haka ita ma Manchester United na matsayi na hudu da maki 38, inda a matsayi na biyar akwai kuwa akwaiTottenham mai maki 33.

Takaddama tsakanin Aljeriya da Maroko a gasar CHAN

Fußball WM Katar | Kroatien v Marokko
'Yan wasan Maroko sun jima suna takun saka da takwarorinsu na AljeriyaHoto: Thanassis Stavrakis/AP/picture alliance

Yanzu ta tabbata cewa 'yan kasar Maroko zakarun kwallon kafa na kofin CHAN na nahiyar Afirka na kwallon da ya kunshi 'yan wasan da suke buga wasa a cikin gida ba za su halarci gasar da kasar Aljeriya za ta dauki nauyi ba, saboda kasar ta Aljeriya taki amincewa jirgin saman 'yan wasan da zai taso daga birnin Rabat fadar gwamnatin Maroko ya sauka kai tsaye a birnin Algiers, sakamakon katse huldar sufurin jirage sama tsakanin kasashe a watan Satumban shekara ta 2021 lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu makwabta ta yi tsami. Tuni Gianni Infantino shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta FIFA da Patrice Motsepe shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka suka fara neman hanyoyiyn sasanta wannan takaddama.

Wa ya haddasa mace-mace a filin wasan Indonesiya?

Indonesien | Nach den Unruhen am Kanjuruhan Stadion
Filin wasa na Kanjuruhan da ke kasar IndonesiyaHoto: Ari Bowo Sucipto/Antara Foto/REUTERS

A kasar Indonesiya, an fara shari'ar mutane biyar da ake tuhuma da sakaci da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 135 yayin da 'yan sanda suka watsa hayaki mai saka hawaye a filin wasan kwallon kafa, abin da ya haifar da tirmutsitsi a watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2022. Shi kansa Shugaba Joko Widodo na kasar na Indonesiya ya kafa kwamitin bincike sakamakon yadda lamarin ya fusata mutane a kasar. Akwai kimanin 'yan kallo 42,000 lokacin wasan kungiyoyin biyu masu hamayya da juna, a filin wasan da ya dace ya dauki kimanin mutane 36,000 kuma rige-rigen neman hanyar fita daga filin wasan lokacin da rikici ya kaure kuma 'yan sanda suka fara harba hayaki mai saka hawaye ya janyo mutuwar kimanin mutane 135. Wannan shi ne  hadari a filin wasa mafi muni da aka taba samu a kasar ta Indonesiya.

Djokovic na halartar gasar tennis ta Ostareliya

Kasachstan Tennis ATP Novak Djokovic
Novak Djokovic ya jima yana jan zare a fagen tennis na duniyaHoto: Stas Filippov/AP Photo/picture alliance

 Bayan da aka tasa keyarsa daga Ostareliya kuma aka hana shi karawa a gasar Tennis na watan Janairun bara, bayan da ya ce ba zai yi allurar rigakafin COVID-19 ba, Novak Djokovic ya dawo bana kuma ya bayyana farin-cikinsa na kasancewa a gasar, tunda a cewarsa ta na kayatar da shi. Sai dai ya ce ba zai taba mantawa da yadda aka tozarta shi ba. Gasar ta bana ta samu halartar manyan ‘yan wasan tennis na duniya.