1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Kammala gasar tennis

Suleiman Babayo LMJ
June 12, 2023

Manchester City ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai a karon farko bayan doke Inter Milan da ci daya mai ban haushi, an kuma kawo karshen gasar tennis ta birnin Paris na kasar Faransa mai tasiri.

https://p.dw.com/p/4STRL
UEFA Champions League | Kofin Zakarun Turai | Manchester City | Inter Mailand
A karon farko tun bayan kafa ta, Manchester City ta lashe kofin zakarun TuraiHoto: MartinxRickett/PA Images/IMAGO

Ana dai fafata da gasar kofin zakarun nahiyar Turan duk shekara, kuma an fafata wasan karshen ne a filin wasa na Atatürk Olympic da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya. Wannan nasara ta kara fitowa fili da karfin da gasar Premier League ta Ingila ke da shi kamar yadda masharhanta suka nunar. Ita dai kungiyar Manchester City ta saka kwallo a raga ana mintoci 68 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ta kafar dan wasanta Rodri mai shekaru 26 da haihuwa dan kasar Spain.
An fara mayar da martani a Amurka bayan da shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Ajentina Lionel Messi wanda yake wasa da kungiyar PSG ta kasra Faransa, ya tabbatar da cewa zai koma kasar da wasa. Messi dai zai taka leda a kungiyar Inter Miami a kan makudan kudi. Haka kuma akwai talla da zai rinka yi wa wasu kamfanoni da zai kara samun kudin shiga.

Kwallon Kafa | Lionel Messi | Inter Miami
Lionel Messi zai koma kungiyar Inter MiamiHoto: Wilfredo Lee/AP Photo/picture alliance
CAF Champions League | Wydad | Al Ahly | Nasara
Al-Ahly ta sake lashe kofin zakarun nahiyar AfirkaHoto: Fadel Senna/AFP/Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahly da ke kasar Masar ta samu nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Afirka, bayan ta doke kungiyar Wydad Casablanca. An dai tashi daga wasan daya da daya, sai dai kuma a fafatawar da suka yi a gida da waje kungiyar ta Al Ahly tana da ci uku yayin da ita kuma kungiyar Wydad take da maki biyu.#b#

Faransa | Tennis | French Open | Novak Djokovic
Zakaran gasar kwallon tennis ta Faransa Novak DjokovicHoto: LISI NIESNER/REUTERS

Bayan kwashe tsawon makonni uku ana fafatawa a gasar tennis a birnin Paris na kasar Faransa da ake kira da Roland Garros ta shekara-shekara, a karshen Novak Djokovic ya yi nasara a bangaren maza yayin da Iga Swiatek ta samu nasara a bangaren mata. Shi dai Djokovic dan kasar Sabiya ya kasance cikin gwanayen wannan wasa na tennis, inda yanzu haka yake kan gaba cikin jerin gwanaye. Haka ita ma Swiatek 'yar kasar Poland, ta kasance wadda yanzu haka take jan zarenta a bangaren na tennis na duniya.

Italiya | Firaminista | Silvio Berlusconi | AC Milan
Marigayi tsohon firaministan Italiya, Silvio BerlusconiHoto: Cecilia Fabiano/LaPresse via ZUMA Press/picture-alliance/dpa

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta Italiya wadda a baya ta lashe gasar Serie A da wasannin kasashen Turai, ta mika jinjina ga wanda ya mallaki kungiyar marigayi tsohon firaministan kasar Silvio Berlusconi. Shi dai Marigayi Berlusconi ya bar duniya yana da shekaru 86 kuma ya kasance daya daga cikin masu arziki na kasar. A cikin wata sanarwa kungiyar ta AC Milan ta ce, ko yaushe za ta tuna da shugabanta Marigayi Silvio Berlusconi wanda ya jagorance ta daga shekarar 1986 zuwa shekara ta 2017. A tsukin wannan lokacin, kungiyar ta lashe kambu 29 da suka hadar da gasar zakarun Turai da kuma lig din Italiya da ake kira da Serie A.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani