1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Makomar Barcelona

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 14, 2023

Akwai yiwuwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta Spaniya, ta fuskanci gagarumar matsala sakamakon tuhumarta da bai wa Kwamitin Alkalan Wasa

https://p.dw.com/p/4OeVZ
Spanien | Barcelona
Barcelona dai na zaman guda cikin fitattun kungiyoyin kwallon kafa a SpainHoto: Manu Fernandez/AP Photo/picture alliance

Hukumar Kula da Harkokin Wasanni ta Spaniya ce dai ta ce ta na shirin daukar mataki a kan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, a ci gaba da fuskantar tuhuma a gaban kuliya da kungiyar ke yi dangane da zargin biyan makudan kudi har tsawon shekaru ga mataimakin Kwamitin Alkalan Wasa na kasar. Shugaban Hukumar Kula da Wasanni ta Spaniya José Manuel Franco ne ya tabbatar da hakan a wata hira da kafar yada labarai ta Channel Telecinco, inda ya ce gwamnati za ta shiga cikin sauran bangarori da ke zargin kungiyar ta Barcelona tare da maka ta a kotu. Ita ma babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid, ta sanar da aniyarta ta shiga a dama da ita domin tabbatar da ganin an hukunta Barcelona. Sai dai Barcelona ta jima tana musanta zargin, inda ma shugabanta Joan Laporta ya ce kungiyar ba ta aikata komai ba kawai dai an hada gangami ne domin bata mata suna. Cikin wani kundi da masu shigar da kara suka fitar wanda kuma kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gani, kungiyar ta Barcelona ta biya kudi da yawansu ya kai miliyan dubu bakwai da 300 daga shekara ta 2001 zuwa 2018.

Bundesliga | FC Union Berlin
Kungiyar kwallon kafa ta Unioin Berlin na ci gaba da barar da damartaHoto: Sören Stache/dpa/picture alliance

An yi ruwar kwallaye a karshen mako, a ci gaba da fafatawa a kakar wasannin Bundesliga ta Jamus ta bana, kamar yadda ta kasance a gasar Premier League ta Ingila. Unioin Berlin ta sake barar da damarta ta ci gaba da kokawar neman matsayi na farko a saman teburin Bundesliga, bayan da ta tashi kunnen doki daya da daya a karawarsu da Wolfsburg. Hoffenheim kuwa kashi ta sha a gidan Freiburg da ci biyu da daya, yayin da Leverkusen ta bi Werder Bremen har gida ta kuma caskara ta da ci uku da biyu. Bochum ta bi Cologne har gida ta kuma lallasa ta da ci biyu da nema. Bayern Munich ta lallasa Augsburg da ci biyar da uku, yayin da RB Leipzig ta yi nasara a gida a kan Borussia Mönchengladbach da ci uku da nema kana aka tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Eintracht Frankfurt da Stuttgart.

Bundesliga | Borussia Dortmund
Ko Borussia Dortmund za ta iya darewa kan teburin Bundesliga nan gaba?Hoto: Jürgen Fromme/firo Sportphoto/picture alliance

Wata kungiya da ta barar da damarta kuwa ita ce Borussia Dortmund da a baya suke tafiya kan-kan-kan in ban da bambancin yawan kwallaye tare da babbar abokiyar hamayyarta Bayern Munich a matsayi na daya da maki 49, inda a karshen mako ta tashi canjaras biyu da biyu a karawarsu da kungiyar Schalke 04 da ke can kasan teburin kakar ta bana a matsayi na 17. Wannan dai shi ne karo na biyu a jere cikin wannan shekara da kungiyar ta Dortmund ta gaza yin nasara, bayan da ta lashe wasanni 10 a jere tun farkon kamawar shekarar ta 2023 da muke ciki. Wasan da tashar DW ta kawo muku tsakanin Hertha Berlin da Mainz kuwa, shi ma an tashi ne kunnen doki daya da daya. Tun da fari dai ana mintuna na 18 da fara wasan kungiyar Hertha Berlin da ke zaman mai masaukin baki ta zura kwallo na farko a raga ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida ta kuma yi ta jan zarenta har sai bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, inda a mintuna na 57 kungiyar Mainz ta bata mata lissafi ta hanyar farke kwallon da aka jefa mata. 

Arsenal | Premier League
Arsenal na ci gaba da jan zarenta a saman teburin Premier League na IngilaHoto: Nick Potts/picture alliance/empics

Idan muka garzaya zuwa gasar Premier League ta Ingila kuwa kungiyar Arsenal na ci gaba da daura damarar lashe kofin gasar ta bana, bayan da ta bi kungiyar FC Fulham har gida ta kuma yi mata dukan kawo wuka da ci uku da nema. Leicester City ta sha kashi a gida a hannun Chelsea da ci uku da daya, an tashi wasa canjaras biyu da biyu tsakanin Leeds United da Brighton, FC Liverpool kuwa da ta yi nasarar lallasa Manchester United da ci bakwai da nema a karshen makon da ya gabata, a karshen wannan mako ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a gidan kungiyar Bournemouth da ke kasan teburun a matsayi na 17. Newcastle United kuwa ta samu nasarar ne a kan kungiyar Wolverhampton da ci biyu da daya yayin da West Ham da Aston Villa suka tashi kunnen doki daya da daya kana Manchester City ta bi Crystal Palace har gida ta kuma caskara ta da ci daya mai ban haushi.

Kwallon Kafa | Senegal | Nasara
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kasar SenegalHoto: Markus Ulmer/ULMER/picture alliance

A gasar cin kofin kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 20 na nahiyar Afirka da aka kammala a karshen mako kuwa, Najeriya ta samu nasarar kasancewa a matsayi na uku bayan da ta lallasa Tunusiya da ci hudu da nema a wasan neman zama na ukun da suka fafata a Masar. A wasan karshe da aka kece raini tsakanin Senegal da Gambiya a ranar Asabar din karshen mako kuwa, Senegal din ce ta samu nasara bayan da ta lallasa Gambiya da ci biyu da nema. Hakan dai ya ba ta nasarar daukar kofin na 'yan kasa da shekaru 20, bayan da ma tuni ta kasance mai rike da kambun kofin na nahiyar Afirka da ta samu nasarar dauka a karon farko a gasar da aka fafata a kasar Kamaru a shekarar da ta gabata ta 2022.