1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni: Waiwayen 2020

Suleiman Babayo LMJ
December 28, 2020

Shirin na wannan lokaci da ke zama na karshe a cikin wannan shekara ta 2020 da muke wa ban kwana, zai duba muhimman abubuwan da suka faru a bangaren wasannin a shekarar da ke karewar.

https://p.dw.com/p/3nHoT
1. Bundesliga 1. FSV Mainz 05 v SV Werder Bremen
Wasanni ba tare da 'yan kallo baHoto: Christian Kaspar-Bartke/Getty Images

Daya daga cikin manyan batutuwan da aka fara samu a farkon shekarar na zaman annobar cutar coronavirus wadda ta faro daga kasar Chaina kuma ta yadu cikin hanzari zuwa sauran sassan duniya, lamarin da ya tilasta dakatar da wasannin a kusan daukacin kasashen duniya, karo na farko a yanayin da ba na yaki ba da kuma ya shafi duniya baki daya.

An kuma soke wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, wato Olympic da aka tsara a birnin Tokyo na kasar Japan, shi ma karon farko a tarihin wasannin zamani da aka soke lokacin da ba na yaki ba a duniya. Daga bisani an sake bude harkokin wasannin karkashin tsauraran dokoki da suka hada da hana 'yan kallo shiga. A gaba annobar ta haifar da tarnaki ta fannin tattalin arzikin wasanni da aka dade ba a gani ba.

FIFA Fußball-WM 2018 in Russland | Nigeria vs. Argentinien | Diego Maradona
Diego Armando Maradona na Ajantina ya kwanta damaHoto: picture-alliance/NurPhoto/R. Jebarah

Wani labarin da ya dauki hankalin duniya shi ne mutuwar tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Ajantina Diego Armando Maradona ranar 25 ga watan Nuwambar wannan shekarar ta 2020, wanda ya shahara a fagen kwallon kafa a duniya. Ya taba zama wanda ya fi kowa tsada a duniya kuma ya karya tarihin kansa ya sake zama wanda ya fi tsada a karo na biyu, abin da babu wani dan wasa da ya sake yin haka a tarihi. Marigayi Maradona wanda ya bar duniya yana da shekaru 60, ya kasance daya daga cikin 'yan wasan kwallon kafa mafiya tasiri a tarihin kwallon kafa na duniya, kuma yana cikin wadanda suka fito da sunan Ajantina idon duniya sakamakon shahara a kwallon kafa.

Lokacin da Maradona ke tsakiyar ganiyarsa, ya jagoranci Ajantina lashe kofin duniya a Mexiko a shekarar 1986. A wannan gasa Maradona ya yi rawar gani da sauya tahirin kwallon kafa har abada. Tuni aka sauya sunan lig-lig da ake karawa a Ajantina zuwa sunan Copa Diego Maradona domin tunawa da marigayin, wanda ya zama mutum da ya fi yin fice a daukacin kasar. Kuma wani dan majalisar dattawan Ajantinan, ya mika bukatar saka hoton Diego Maradona a daya daga cikin takardun kudin kasar.

Senegalesicher Fußballer Papa Bouba Diop
Rashin gwarzon dan wasan Senegal Papa Bouba Diop Hoto: ANE Edition/imago images

Shi ma Papa Bouba Diop dan wasan kwallon kafa na kasar Senegal wanda ya taka rawar gani da jefa daya daga cikin kwallayen da suka sauya tarihi a wasan cin kofin kwallon kafa na duniya a shekara ta 2002, inda ya ci kwallo daya tilo da Senegal ta doke Faransa lokacin bude wannan gasa ta 2002, kuma lokacin da Faransa take rike da kofin na duniya bayan lashe gasar shekarar 1998.

Papa Bouba Diop ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 42 a duniya, kuma ana daukarsa a matsayin gwarzo. Shi dai Maraigayi Diop da ya zama gwarzo a kasarsa ta Senegal ya yi wasa a kungiyoyin Lens da Fulham da West Ham United da kuma Birmingham City na kasar Ingila.