1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanki ya koma ruwa a Sudan ta Kudu

February 18, 2014

Faɗa ya sake ɓarkewa a ƙasar tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye duk da yarjejeniyar dakatar da buɗe wutar da aka cimma tsakanin sassan biyu.

https://p.dw.com/p/1BB0h
Südsudan Soldaten 14.01.2014 in Juba
Hoto: Charles Lomodong/AFP/Getty Images

An ba da rahoton cewar dakarun da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu Riek Machar sun kai wani hari a garin Malakal mai arzikin man fetur. Masu aiko da rahotannin sun ce ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin dakarun gwamnatin da na 'yan tawayen a gewayen garin da ke a yankin yammaci.

Wannan ita ce karawa ta farko da aka yi tsakanin 'yan tawayen da dakarun gwamnatin,tun lokacin da ɓangarorin biyu suka rataɓa hannu a kan wata yarjejeniyar tsaigata buɗe wuta a cikin watan Janairun da ya gabata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh