1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaRuwanda

An kaddamar da yakin neman zabe a Ruwanda

Abdourahamane Hassane
June 24, 2024

Wani turmutsitsi ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da raunata wasu 37 a a garin Rubavu da ke arewa maso yammacin Rwanda a yayin wani taron gagami da jam'iyyar shugaba Paul Kagame ta gudanar.

https://p.dw.com/p/4hREU
Hoto: Jean Bizimana/REUTERS

 An gudanar da wannan gangami ne makonni uku gabanin zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 15 ga watan Yuli. wanda ake ganin  kagamen shi ne zai samu nasara. Shugaba Paul Kagame, wanda ya shafe shekaru 24 yana mulki, ya gudanar da taron gangami na farko a gundumar Musenze da ke a arewamaso yammacin Ruwanda,a wani filin wasa da ke cike da dimbin magoya bayansa, a lokacin bude yakin neman zabe a hukumance. Majalisar dokokin Ruwanda ta zabi Paul Kagame a matsayin shugaban kasa bayan da Pasto Bizimungu ya yi murabus a shekara ta   2000.