SiyasaTurai
Wani dan bindiga ya kashe mutane biyar a Croatia
July 22, 2024Talla
Kafar yada labarai ta HRT ta ce dan bindiga da ba a san ko wane ne ba, ya shiga wani gidan kula da tsofaffi da ke garin Daruvar, mai tazarar kilomita 130 daga gabashin Zagreb, ya fara harbi.
Akalla mutane biyar ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harbin. Majiyar ta ce wanda ake zargin ya gudu amma daga baya ‘yan sanda suka kama shi.
Croatia ta yi yakin neman 'yancin kai a lokacin ballewar Yugoslavia daga 1991 zuwa 1995. A bara a makwabciyarta Serbia, ta fuskanci hare-haren wuce gona da iri, ciki har da kisan kiyashi a wata makaranta da ke babban birnin Belgrade inda mutane 10 suka mutu.