Wani bangare marasa kyau na alawar cakuleti
Lokacin Kirsimeti lokaci ne amfani da alawar cakuleti wadda ake samar da ita daga cocoa wanda yara kan yi nomansa don sama wa iyayensu kudin shiga. Sai dai ana nuna damuwa kan ci da gumin irin wadannan yaran.
Rashin sanin sirrin da ke boye
Mutane na sayen alawar cakuleti ba tare da sanin irin matakan da aka bi wajen samar da cocoa din da aka yi ta ba. Wannan ne ya sa kamfanin Nestle da ke yi cakuleti ya ce ba ya sayen cocoa har sai ya tantance cewar ba a yi amfani da kananan yara wajen nomansa ba saboda irin damuwar da ya ke da ita ta ci da gumin yara da ake wajen noman na cocoa.
'Yar shekarar 9 da ke noman cocoa
Moahe mai shekaru 9 da haihuwa ta shafe tsawon lokaci tana yin feshin kwari da ban ruwa a gonar cocoa ta mahaifinta. A kullum ta kan jawo ruwa daga wata rijiya da ke kauyensu don yin ban ruwa. Moahe guda ce daga cikin yara miliyan 2 da ke aiki a gonakin cocoa da ke yammacin Afirka.
Manomin Cocoa
Wannan shi ne Fabrice Amangoua a kofar gidansa da ke kauyensu a kasar Ivory Coast. Fabrice dai manomin cocoa ne kana mahaifin Moahe. Mutumin na noma eka 3 na cocoa. Yabanyar da aka samu a baya-bayan nan ta sanya faduwar farashin cocoa a duniya wanda hakan bai yi wa Fabrice dadi ba.
Cocoa din da bai nuna ba
Farin wata sha kallo: Nan cocoa ne a wata gona da ke kasar Ivory Coast a yankin yammacin Afirka. Yankin shi ne kan gaba wajen samar da cocoa a duniya. Kashi 75 cikin 100 na cocoa din da ake samu a duniya kan fito ne daga nahiyar Afirka.
Tabbatgar da ingancin cocoa
A kan yawaita duba tare da tabbatar da ingancin cocoa don tabbatar da ingancinsa musamman ma idan ana magana ta danshi. Kwari da hunhuna kan yi illa babba ga cocoa ko kuma lalata dandanonsa.
Busar da cocoa da rana mai zafi
Samar da alawar cakuleti na da wuya. Bayan girbi a kan busar da cocoa sannan a killace shi cikin buhunhuna kafin a fice da shi zuwa wasu nahiyoyin. Kamfanin Nestle na sayen kimanin tan dubu 47 na cocoa da aka noma ba tare da amfani da kananan yara ba.
Ilimantarwa kan illar sanya yara aikin karfi
Serge da ke aiki da kungiyar nan ta ICI mai nasaba da harkar noman cocoa na ilimantar da mutane kan illar sanya yara kanana aikin karfi. Wannan aiki nasa na kokarin game ko ina. Sai dai zai iya fuskantar koma-baya musamman daga iyayen yaran da ake sanya aikin karfi.