Wani alikoftan Amirka yayi hadari a Afghanistan
May 6, 2006Talla
Wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojin Amirka ya yi hatsari a Afghanistan. Alikoptan yakin dai ya yi hatsari ne a lokacin da yake kai farmaki. Kawo yanzu ba´a san makoma sojojin Amirka 10 dake cikin jirgin ba, kana kuma ba´a san musabbabin hatsarin ba. To amma rundunar sojin Amirka a Afghanistan ta ce ba abokan gaba suka harbo jirgin ba.