1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Volker Perthes ya fice daga kasar Sudan

Binta Aliyu Zurmi
September 14, 2023

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan Volker Perthes wanda a baya sojojin da ke rike da madafun iko suka sanar da yanke mu'amala da shi ya yi murabus.

https://p.dw.com/p/4WLEJ
USA UN l Sonderbeauftragter des Generalsekretärs der Vereinten Nationen für Sudan,  Volker Perthes
Hoto: Eskinder Debebe/UN/Xinhua/IMAGO

Volker Perthes wanda ya sanar da ajiye aikin nasa a jiya Laraba a zauren taron kwamitin tsaro na Majalisar, ya yi gargadincewar rikicin da yanzu haka ke ci gaba da ruruwa wanda kuma ba a hango karshen shi ba a kasar ta Sudan ka iya zarcewa ga mumunan yakin basasa. 

Jakadan ya kara cewa tuni yankin Dafur ya zama wani fagen daga a tsakanin mabanbanta kabilu.

Tun a tsakiyar watan Afrilun da ya gabata ne dai sojojin kasar Sudan da kuma rundunar sa kai ta RSF karkashin jagorancin tshohon mataimakin shugaban kasa Mohamad Hamdan Daglo suka fara kai wa juna hare-hare.

Ko a ranar Laraba Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Shugaban Mulkin Sojin Sudan Abdel Fattah al Burhan a  Turkiyya, ziyarar da ke zama irinta ta biyar da al Burhan ya kai  kasar tun bayan da yaki ya barke.