1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka rasu a girgizar kasa sun haura 15000

Mahmud Yaya Azare
February 8, 2023

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a girgizar kasar Turkiyya da Siriya sun haura mutum 15000 a waje guda kuma hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce mutanen da iftila'in ya shafa za su kai mutane miliyan 23

https://p.dw.com/p/4NExz
Türkei | Erdbeben
Hoto: Suhaib Salem/REUTERS

A yayin da aka shiga yini na hudu na girgizar kasar da aka baiyana da mafi karfi a tsawon shekaru, ma'aikatan lafiya dana agaji na ci gaba da aikin ceton mutanen da suka makale a cikin buraguzai. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce mutanen da wannan girgigizar kasar ta shafa a Turkiyya da Siriya za su kai kimanin mutane miliyan 23 a kasashen biyu.

Shugaban sashen agaji na hukumar ta WHO Adelheid Marschang ya ce girgizar kasar ta lallata asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya wanda ke nuna tsananin bukatar agaji ta fuskar lafiyar da kasashen biyu ke da shi a yanzu.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a garin Kahramanmaras
Hoto: Mustafa Kamaci /AA/picture alliance

Shugaban Turkiya Raceip Erdogan wanda ya kai ziyara Kahraman inda girgizar kasar ta fi kamari, ya sanar da dokar ta baci a jihohin da iftila'in ya shafa.

"Ba zamu bar ko mutum daya cikin wannan tsananin sanyi ba tare da mun samar masa da sabon matsuguni ba. Za kuma mu bayar da tallafin kudi ga duk wadanda wannan iftila'in ya ritsa dasu. Ma'aikatan ceto na Turkiyya da na kasashen duniya na ci gaba da ceton rayuka. Muna cike da fatan samun karin wadanda ke da rai daga cikin buraguzan."

A waje guda kuma an shawo kan gobarar da ta tashi a tashar jirgin ruwa ta Iskandron na Turkiyya, inda ake sauke kayyakin agaji da makamashi.

Wasu 'yan Siriya ke aikin taimakon jinkai bayan girgizar kasa
Hoto: KHALIL ASHAWI/REUTERS

A yankin arewacin Siriya an kuma samun girgizar kasa a wannana Laraba wandda ya kara jawo karin rushewar gidaje. Wata ma'aikaciyar jinya da ta isa yankin Hama da a baya ma'ikakatan agaji na kasa da kasa suka kaurace wa saboda takunkumin da aka kakabawa Siriya,ta ce halin da ake ciki a yankin yayi muni matuka.

An dai yi nasarar ceto mutane kimanin dubu 12 da 400 a aikin ceton da zakulo mutane daga buraguzai, kamar yadda aka sanar da kafa tantuna dubu takwas a yankin Ainul Arab don sake tsugunar da mutanen da tsananin sanyi ke addabansu.