1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

131211 UN Westerwelle

Usman ShehuDecember 13, 2011

Rahoton da hukumar kare yancin Bi'adama ta MDD ya fitar, ya bayyana irin munin da rikicin Siriya ya kai, inda aka yi kiyasin mutane 5000 suka mutu.

https://p.dw.com/p/13RlK
epa03002378 Syrian and Turkish protestors shouts slogans against Syrian President Bashar Assad holding Syrian flags during a demonstration at Taksim Square in Istanbul, Turkey 13 November 2011. Reports state that hundreds of Syrian government supporters attacked the Turkish Embassy in Damascus on 12 November after the Arab League voted to suspend Syria from its meetings and impose sanctions against the Syrian regime over its failure to end crackdown on pro-democracy protesters, Anadolu Agency reported. EPA/TOLGA BOZOGLU +++(c) dpa - Bildfunk+++
Masu boren adawa da gwamnatin SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

Bayan rahoton da MDD ta fitar bisa halin da ake ciki a kasar Siriya, an gano yawan wadanda suka mutu a rikicin kasar ya zarta na da kamar yadda majalisar ta sanar. Don haka ne ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya zartas da kuduri kan rikicin na Siriya, bayan ganawar da ya yi da kwamishiniyar kare yancin Bil'adama na majalsar a birnin New York kan cin zarafin Bil'adama da ake yi a Siriya.

Jikkata mutanen da dakarun gwamnati Bashar Al-Assad suka yi kan masu boren neman a kifar da gwamnatinsa sai kara samun bayanai kan kamarin da lamari ke yi ake ji. Kamar dai yadda kwamishiniyar kare yancin Bil-adama ta MDD Navi Pillay ta shaidawa kwamitin sulhu na MDD, inda a kiyasinta tace kimanin mutane dubu 5000 suka hallaka a rikicin na Siriya, yayinda aka tsare kiminin mutane 14000, kana a fadara ta 'yan gudun hijira da suka tserewa rikicin sun kai kimanin 12,400. Pillay ta bayyana yadda wadanda aka tsare ke mutuwa

Außenminister Guido Westerwelle (FDP) begruesst am Montag (12.12.11) in New York (USA) die Hohe Kommissarin der Vereinten Nationen fuer Menschenrechte (UNHCHR), Navi Pillay. Die Zahl der Todesopfer bei den Protesten in Syrien ist deutlich gestiegen. "Wir muessen davon ausgehen, dass etwa 5.000 Menschen bereits ihr Leben gelassen haben", sagte Aussenminister Guido Westerwelle am Montag nach dem Treffen mit Pillay in New York. Bislang hatten die Vereinten Nationen die Zahl der Todesopfer auf 4.000 geschaetzt. (zu dapd-Text) Foto: Oliver Lang/dapd
Navi Pillay kwamishiniyar kare yancin Bil'adama da Guido Westerwelle mi nistan harkokin wajen Jamus a New YorkHoto: dapd

"Wannan ya kara bayyana mana gaskiyar cin zarafin mutane da ake yi, don haka na ke bada shawar kwamitin sulhu da ya mika lamarin ga kotu kasa da kasa da ke hukunta man'yan laifuka wanda ke da zama a birnin Hague"

Jawabin da akaji daga bakin Pillay dai ya tada hankulan wakilan zauren majalisar, bisa munin tashin hankalin na kasar Siriya, inda ta bayyana mummunan yanayin da aka shiga a kasar. Gabanin kwamishiniyar kare yancin Bil'adama ta gabatar da jawabinta, sun gana da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle. Shi ma kansa Westerwelle ya yi tsokaci kan tashin hankalin dake faruwa a kasar Siriya.

"Kimanin mutane 5000 suka mutu daga bangaren farar hula, ba za a lamunta da hakan ba, lamarin yana bukatar martanin kasa da kasa"

Westerwelle ya yi maraba da bin sahun kasashen EU da kwamitin sulhu ya yi, kana ya kara jadda matsayin Jamus wajen ganin ta hada kan wakilan kwamitin sulhu na MDD 15, don su amince da zartas da kuduri kan gwamnati Al-Assad. Ba tare da kiran suna ba, ministan harkokin wajen Jamus yace duk kasar da ke goyon bayan Siriya, kamata yi ta sauyi tunani.

"Ina fatan rahoton ya sauya ra'ayin wasu a kwamitin sulhun, don haka za a samu martanin bai daya daga kasashen duniya, kan wannan zalumci da ake yi"

Syrian President Bashar Assad (R) meets with Russian Foreign Minister Sergei Lavrov (L) at the Ash-Shaeb presidential palace in Damascus, Syria, 20 March 2008 Sergei Lavrov is in Damascus for talks on the Middle East peace process, Iraq, Lebanon and the Palestinian issue. EPA/YOUSSEF BADAWI +++(c) dpa - Report+++
Shugaban kasar Siriya a lokacin da yake ganawa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei LavrovHoto: picture-alliance/dpa

Duk haka dai kasashen China da Rasha sun jaddada kare gwamnatin Siriya, musamman Rasha duk da mutuwar dubban mutane, amma tana sukan rahoton, tana mai marawa abokiyarta gwamnatin Siriya. A watan Oktoba tare da hadin gwiwar China, kasashen biyu suka yi amfanin da karfinsu a majalisar wajen hana kudurin da aka yi akan Siriya. Duk da cewa an kudurin baya dauke da abinda wakilan EU suka so a yi, na azawa Siriya takunkumi.

Jakadan Rasha a MDD yace rahoton da kwamishiniyar kare yancin Bil'adama na majalisar ta bayar kan Siriya an yi karin gishiri, inda ya yi gargadin cewa duk wani harin kan Siriya daga kasashen waje, to kara zubar da jini ne kawai zai jawo.

Mawallafa: Thomas Schmidt da Usman Shehu Usman

Edita:         Zainab Mohammed Abubakar