1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa'adin da ƙungiyar Larabawa ta ƙayyadewa Siriya ya cika

November 16, 2011

Aau laraba ne wa'adin da ƙungiyar Larabawa ta ƙayyade wa Siriya ke cika domin gwamnati ta dakatar da aiwatar da ƙarfin bindiga kan 'yan adawa ko kuwa a kori Siriyar daga ƙungiyar

https://p.dw.com/p/13BVK
Tankokin yaƙin Siriya dake fafutukar murƙushe 'yan zanga-zangar adawa da gwamnatiHoto: picture alliance/dpa

Shin a haƙiƙa kuwa za a kori Siriya daga ƙungiyar ta haɗin kan Larabawa ko kuwa? Wannan dai ita ce ayar tambayar da ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar zasu nemi amsarta a yau laraba, a zaman taronsu na musamman a Rabat, fadar mulkin ƙasar Moroko. Muddin shugaba Bashar al-Assad bai gabatar da wasu cikakkun bayanai game da azamarsa ta kawo ƙarshen matakan muzantawa akan farar fula ba, wajibi ne su yi na'am da shawarar korar Siriyar.

Amma kuma mai yiwuwa lamarin yayi daura da hakan ya ɗauki wata sabuwar alƙibla. Domin kuwa muddin shugaba Assad ya amince da karɓar baƙoncin tawagar wakilan masu fafutukar kare 'yancin ɗan-Adam su 500 da na ƙungiyar ƙungiyar ƙasashen Larabawa, hakan zata wadatar a game da canza shawarar dakatar da wakilcin Siriyar a ƙungiyar. Ga dai abin da sakatare-janar na ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa Nabil al-Araby ke cewa:

Arabische Liga Ägypten Nabil al-Arabi
Sakatare-janar na ƙungiyar Larabawa kuma ministan harkokin wajen ƙasar Masar Nabil al-ArabiHoto: picture alliance/dpa

"An yi wata ganawa tsakanin ƙungiyar haɗin kan Larabawa da ƙungiyoyi 16 dake fafutukar kare haƙƙin ɗan-Adam. A tattanawar an tsayar da shawarar cewa kowace ƙungiya na da ikon tura wakilanta zuwa Siriya, muddin hakan ta tabbata a yau laraba. Dukkansu sun bayyana ƙaunar shiga a dama da su kuma suna da cikakkiyar masaniya game da irin waɗannan abubuwa. Na kuma sikankance cewar majalisar ministoci, a zamanta na Rabat zata amince da hakan ta yadda za a fara wannan manzancin nan take."

Wani ƙwararren masani akan al'amuran haƙƙin ɗan-Adam na tattare da ra'ayin cewar tura tawagar zai taimaka a samu kafar kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a ƙasar Siriya kuma kafofin yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewar gwamnati a shirye take ta karɓi baƙoncin tawagar. Bisa ga dukkan alamu kuwa ƙungiyar ta ƙasashen Larabawa tana tsaye akan bakanta a game da shawarar da ta tsayar, wataƙila sakamakon matakan takunkumin da ƙungiyar tarayyar Turai ta ƙaƙaba wa Siriyar. Wasu rahotanni dai sun ce ƙungiyar ta nema daga 'yan adawar da su fara tanadar da wani takamaiman shiri na karɓar akalar mulki, amma ba a hukumance ba. Ƙungiyar fafutukar neman demokraɗiyya a ƙasar ta Siriya tana daɗa samun amincewa ta ƙasa da ƙasa. Shugaban majalisar 'yan adawar Burhan Ghalioun ya gana da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle tun a ranar litinin da ta wuce, kuma a jiya talata aka karɓi baƙuncinsa a hukumance a birnin Mosko: Ghalioun ya ce wajibi ne Rasha ta ba da goyan baya ga matsin lambar ƙasa da ƙasa akan shugaba Assad:

Syrien Opposition Nationalrat Damaskus
Wakilan majalisar 'yan adawa ta SiriyaHoto: picture alliance/dpa

"Muna sha'awar tattaunawa da wasu ɓangarori na gwamnati da ba su da hannu a ta'asar zub da jinin dake wakana. Tun da farkon fati muka nuna cewar ba mu ƙyamar irin wannan tattaunawa. A maimakon haka ma dai muna sha'awar tattauna maganar miƙa mulkin ne a cikin ruwan sanyi domin gudun katsalandan soja ko wani yaƙi na basasa."

Bayan ganawarsa da mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Michail Bogdanov, shugaban 'yan hamayyar yayi nuni da cewar karɓar baƙuncinsa da gwamnatin Rasha tayi na mai yin nuni ne da irin matsin lambar da shugaba Assad ke fuskanta yanzu haka.

Mawallafi: Björn Blaschke/Ahmad tijani Lawal

Edita: Zainab Muhammed Ahmed