1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ursula Von der Leyen ta zama sabuwar shugabar kungiyar EU

Abdoulaye Mamane Amadou
July 2, 2019

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun cimma matsaya a kan nadin wasu muhimman mukamai na jan ragamar kungiyar tarayyar Turai a yayin babban taronsu karo na biyu a kasar Beljiyam.

https://p.dw.com/p/3LTkd
Ursula von der Leyen CDU Verteidigungsministerin Deutschland
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Shugabannin sun zabi Ursula von der Leyen ministar tsaron kasar Jamus a matsayin sabuwar shugabar kungiyar a dazu yayin da ita kuwa Christine Lagarde ta hukumar bayar da lamuni ta IMF za ta rike mukamin shugabar babban bankin taryyar Tura BCE.

Baya ga Ursula da Lagarde, shugabannin 28 sun kuma zabi firaministan Beljiyam Charles Michel a matsayin shugaban hukumar a yayin da Josep Borrell babban jami'in huldar diflomasiyar kasar zai ja ragamar ma'aikatar harkokin diflomasiyar kungiyar ta EU inda zai maye gurbin Frederica Mogreni da ta rike mukamin a can baya.