An shirya zaman taron shawo kan rikicin siyasa
February 7, 2019Talla
An shirya zaman taron ne, bayan da ake ci gaba da ja-in-ja a tsakanin Shugaba Nicolas Maduro da jagoran Adawa Juan Guaido kan madafun iko. Zaman zai gudana a birnin Montevideo na kasar Uruguay, don duba hanyar da za a bi don samar da maslaha da kuma damar isar da kayyakin agaji, bayan da aka zargi sojoji da laifin rufe kan iyakar kasar da kasar Kolombiya.
Rikicin shugabanci a Venezuelan, ya raba kan kasashen duniya, inda kasashen Amirka, Faransa da Jamus da Spaniya da Kanada da kuma Ostireliya ke nuna goyon bayansu ga jagoran adawa Juan Guido da ya ayyana kansa a matsayin shugaba na riko, a yayin da Rasha da Chaina ke tsayin daka ga Shugaba Nicolas Maduro.