1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Fargabar UNICEF kan tallafa wa yara

August 21, 2023

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce sama yara miliyan biyu a Nijar na bukar agaji yayin da kasar ta fada cikin dambarwar juyin mulki baya ga dama tana tsaka da matsalar 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/4VPVC
Tambarin Asusun Unicef a ofishinsa da ke Geneva
Asusun Unicef ya nuna damuwa game da halin da yara ke ciki a NijarHoto: Denis Balibouse/REUTERS

A cikin sanarwar da ya fidda a wannan Litinin Asusun ya yi shelar cewa kafin juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 27 ga watan Yuli dama yara 'yan kasa da shekaru biyar miliyan guda da rabi a Nijar na fama da cutar tamowa sannan kuma wasu dubu 430 na fama da matsanancin nau'i na cutar.

UNICEF ya kuma kara da cewa katse wutar lantarki da Najeriya ta yi biyo bayan matakin matsa lamba ga sojojin da suka kifar da gwamnati da ECOWAS ta dauka ya kara dagula al'amura tare kuma da haifar da barazanar lalacewar alluran da aka tanadar a asibitotcin kasar domin kula da yara.

Karin bayani: Tamowa na barazana ga rayuwar kananan yara

Asusun ya yi kira ga masu ruwa da tsakki a kan dambarwar juyin mulkin Nijar da su gaggauta buda wa ma'aikatansa kofofin shiga Nijar domin isar da kayan agaji da suka makale a kan iyakokin kasar tare kuma da kiran masu hannu da shuni da kadda su katse tallafin da suke ba wa Nijar a fannin kula da yara.