1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNHCR: 'Yan gudun hijira na bukatar kariya

Pinado Abdu WabaAugust 24, 2015

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta yi kira ga Turai da ta samar da mataki na saukake matsalar tudadowar baki.

https://p.dw.com/p/1GKgJ
Flüchtlinge Mazedonien Griechenland Grenze
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Licovski

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta yi kira ga Turai da su hada kai su samar da mataki na bai daya don tinkarar matsalar tudadowar 'yan gudun hijira, musamman saboda abubuwan da suka faru a kasashen Girka, Masadoniya da Serbiya a karshen makon da ya gabata.

A wata sanarwar da ta fitar hukumar ta ce ana bukatar karin taimako wajen kare lafiyar masu gudun hijirar a yayin da suke kokarin zuwa sauran kasashen Turan.

A daren lahadi kadai, ana kiyasin cewa mutane 7000 ne suka shiga Serbiya bayan da makociyarta Masadoniya ta bude iyakokinta sakamakon matsin lambar da ta fiskanta a dalilin arangamar da ta barke tsakanin 'yan sandata da masu gudun hijirar.

Ita dai hukumar ta UNHCR ta ce zata gina karin wuraren tarbar masu neman mafakan a kan iyakokin wadannan kasahen, sannan ta kuma nuna fushinta ga gwamnatin Girka, wadanda ta ce ba su yi rajistar mutanen kafin suka ratsa zuwa Masadoniyar ba.