1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNCHR ta ja hankali kan 'yan gudun hijirar Siriya

Ramatu Garba Baba
July 5, 2018

Fadan da a ke yi a Siriyia na barazana ga rayuwar mutum fiye da 750,000 inji shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filipo Grandi, inda ya nemi a tsagaita bude wuta don isar da agaji.

https://p.dw.com/p/30tyR
Syrien Flüchtlinge aus dem Irak in Damaskus
Hoto: AP

Babban jami'in majalisar Grandi, ya ce akwai wadanda ke cikin tsaka mai wuya da ke bukatar taimakon gaggawa a sanadiyar raunin da suka ji, ya ce kamata ya yi masu fada da juna su tsagaita bude wuta don bai wa jami'ai damar kwashe su don yi musu magani.

Ya kuma yi kira na neman taimakon kasar Jordan, kan ta bude kofofinta don bai wa wadanda rikicin Siriyan ya shafa shiga kasar,  Mista Grandi ya ce sauran kasashen duniya, su tallafawa kasar ta Jordan da kudi don daukar dawainiyar 'yan gudun hijirar.