1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine za ta maida martani kan wadanda suka harbo jirgin sojinta

June 14, 2014

'Yan awaren Ukraine suka kakkabo jirgin sojin kasar lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama da ke Luhansk a gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1CIIo
Ukraine Flugzeugabschuss 14.6.2014
Hoto: REUTERS

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce gwamnati za ta maida martani kakkausa kan 'yan awaren da suka harbo jigin sojin kasar na dakon kaya wanda ya ke dauke da kimanin soji 49 wadanda dukanninsu sun rasu.

Shugaba Poroshenko ya ce shakka babu Ukraine za ta bi dukannin matakan da suka kamata don hukunta wadanda suka kai wannan hari wanda ya ce na ta'addanci ne duk da cewar gwamnatinsa ta masu rajin ganin an samu zaman lafiya ce a kasar.

Wadannan kalamai na Mr. Poroshenko dai na zuwa ne bayan da ya yi wata ganawa ta gaggawa da manyan jami'an tsaron kasar a birnin Kiev da sanyin safiyar ranar Asabar domin sanin irin matakan da ya dace su dauka.

Harin dai na zuwa ne daidai lokacin da ake zargin Rasha ta bai wa 'yan awaren da ke goyon bayanta makamai.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal