1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta tsige babban kwamandan sojin kasar

February 9, 2024

Ma'aikatar tsaron Ukraine ta ce an tsige babban kwamandan sojojin kasar Valerii Zaluzhnyi daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/4cCud
Hoto: Ukrainian Presidentia/ZUMA//IMAGO

Shugaba Volodmyr Zelenskyy ya wallafa cewa, ya gana da babban kwamandan inda ya bayyana masa cewa, lokaci ya yi da zai bayar da dama ga wani domin ya jagoranci rundunar sojin kasar saboda akwai bukatar a sauya fasalinta, sai dai a cewarsa, Zaluzhnyi zai ci gaba da kasancewa a rundunar.

Tuni dai shugaba Zelenskyy ya nada Oleksandr Syrskyi a matsayin wanda zai maye gurbin Zaluzhnyi. Jim kadan bayan sanarwar, kasar Amirka ta bayyana aniyarta na yin aiki kafa-da-kada da sabon jagoran sojin.

Ana dai ganin sauya babban kwamandan sojin kasar baya rasa nasaba da tsamin dangantaka da ta shiga tsakanin Zaluzhnyi da kuma Shugaba Zelenskyy tun bayan da Ukraine ta yi rashin nasara a hare-haren ramuwar gayya kan Rasha da ta kai a shekarar bara.