1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta bukaci EU ta ba ta gurbi a cikinta

Binta Aliyu Zurmi MNA
March 1, 2022

A yayin da mahukunta a Ukraine ke kokarin ganin sun sami shiga kungiyar Tarayyar Turai, a hannu daya yaki na ci gaba da kankama tsakanin kasar da Rasha.

https://p.dw.com/p/47pd1
Majalisa EU | Brussels | Zelensky
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci EU ta gaggauta daukar kasarsa a cikintaHoto: Jonas Roosens/picture alliance/dpa/BELGA

A ganawar gaggawa da ta gudana ta kafar bidiyo da shugabannin kugiyar Tarayyar Turai da Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine a wannan Talata, shugaban na Ukraine ya bukaci kasashe membobin kungiyar EU da su nuna cewa da gaske suna tare da Ukraine a yaki da take yi da kasar Rasha, ta hanyar ba su kujera a kungiyar. Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da a hukumance Shugaba Zelensky ya aike wa kungiyar ta EU a rubuce takardar neman samun gurbi a cikin kungiyar.

"Kasancewa ba ma cikinku, kasar Ukraine za ta zama ita kadai, mun yi duk iya yinmu na nuna bajintarmnu da ma cancantar zama a wannan kungiya, yanzu muna son ku nuna cewa kuna tare da mu a zahiri, ta hanyar tabbatar mana da cewa ba za ku barmu mu gushe ba. Muna son ku nuna mana cewa ku Turawa ne na asali, ta haka za mu yi nasara a kan makiyanmu."

Majalisar EU | Brusselse
Jawabin Zelensky ta kafar bidiyo ga majalisar EU ya samu jinjina da karbuwaHoto: Jonas Roosens/AFP/Getty Images

Ko kafin wadannan kalamai na Shugaba Zelensky da za a iya cewa sun sosa ran wadanda ke wannan zauren taro, ga baki daya majalisar ta jinjina masa ta kuma una masa goyon baya. Yawacin wakilan majaisar sun saka riguna da aka rubuta "muna tare da Ukraine" a jiki. Da alama za a iya cewa mafarkin Ukraine na shiga kungiyar tarayyar Turai na gab da tabbata. Sai dai shugabar hukumar gudanarwar kungiyar Ursula von der Leyen ta ce wuka da nama na a hannu membobin kungiyar. Amma dai wannan hali da Ukraine ke ciki ya kara karfafa dangantakarsu, inda ta kuma kara da cewa.

"Shugaba Volodymyr Zelensky da al'ummarsa sun zama abin alfahari kuma mutanen da za a yi koyi da su, a rubuce ya tabbatar mana da bukatarsu ta shiga kungiyar nan, kuma tabbas kasar Ukraine da kungiyar EU mun kara kusanci da juna a wannan lokaci. Ina ganin babu wanda a cikin wannan zauren zai ja da irin jajircewar da suka yi a kan manufofinmu, a sabili da haka ya ku 'yan majalisa ina ganin sun cancanci zama a cikin wannan kungiya."

Ya zuwa yanzu dai kasashen duniya na ci gaba da kakaba wa Rasha takunkumai a jerin matakan da suke dauka kan Rasha. Sai dai su ma a nasu bangaren sun tabbatar da Rashar ba za ta kyale su ba, inda suka ce suna daukan matakan zama a cikin shirin ko ta kwana.

Sojojin Ukraine a birnin Kyiv
Sojojin Ukraine a birnin Kyiv na neman ababan fashewa da ba su tashi ba a harin da Rasha ta kaiHoto: Sergei Supinsky/AFP

A Ukraine kuwa dakarun sojin Rasha na ci gaba da luguden wuta, inda a wannan Talata suka kai wani hari a kan anguwannin fararen hula, harin da aka tabbatar ya yi sanadin mutuwar mutane goma ciki har da 'yan kasashen ketare. Kuma Rashar ta yi alkawarin ci gaba da kai wadannan hare-haren har sai an cimma matsaya.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci mahukuntan fadar Kremlin da su gaggauta kawo karshen wannan yakin da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula.

"Ana ci gaba da amfani da bakin bindiga, amma dai hanyar tattaunawa dole ta kasance a bude, hawa teburin sulhu domin duba duk bangarorin cikin lalama zai zama mafi a'ala."

A nata bangaren kungiyar tsaro ta NATO ta sha alwashin kare duk kasashenta daga wani hari da ka iya da Rasha ka iya kai musu, kuma ta yi alkawarin taimaka wa kasar Ukraine. Da yake tsokaci a game da barazanar sa makaman nukiliyarta cikin shirin ko takwana da Rasha ta yi, sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyarsa ba ta da makaman nukiliya, amma "kasashe membobinta uku  wato Amirka da Birtaniya da kuma Faransa sun mallaki makaman nukiliya saboda haka za su kare kansu."

Yanzu haka dai dakarun Rasha na dab da shiga babban birnin kasar Ukraine, Kyiv, inda suka kai harin bam a kan tashar talabijin mallakar gwamnatin Ukraine.