1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta kai harin jirage marasa matuka kan Rasha

June 23, 2024

Hukumomin Rasha sun ce, Ukraine ta kaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuka kan Rasha, ciki har da yammacin yankin Bryansk da ke kan iyakar Ukraine da Belarus.

https://p.dw.com/p/4hPNr
Ukraine ta kai hare-haren jirage marasa matuka kan Rasha
Ukraine ta kai hare-haren jirage marasa matuka kan RashaHoto: STATE EMERGENCY SERVICE OF UKRAINE/REUTERS

Gwamnan yankin Bryank, Alexander Bogomaz ya ce an kakkabo jiragen marasa matuka fiye da 30 da Ukraine ta harba kan yankin da ma wasu yankunan Rasha. Hare-haren na Ukraine na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Rasha ta kai wa Ukraine harin bam da ya lalata wani gini a Kharkiv, birnin na biyu mafi girma a Ukraine, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3 yayin da wasu 56 suka jikkata.

Karin bayani: Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine sun salwantar da rayuka

Har wa yau Rasha ta ce Ukraine ta yi amfani da wasu makamai masu linzami da Amirka ta bata wajen kai hari yankin Crimea, inda nan ma wasu mutum uku suka rasa rayukansu. Har kawo yanzu Ukraine ba ta ce uffan ba kan dukannin hare-haren.