1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta jaddada aniyarta ta tattauna da Rasha

July 25, 2024

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana fatansa game da yuwuwar samun ci gaban diflomasiyya da ma aniyar kawo karshen yakin kasarsa.

https://p.dw.com/p/4ii2S
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba da takwaransa na Chaina
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba da takwaransa na ChainaHoto: Lu Hanxin/AP/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana fatansa game da yuwuwar samun ci gaban diflomasiyya bayan ziyarar da ministan harkokin wajen kasarsa Dmytro Kuleba ya kai kasar Chaina. Zelensky ya bayyana a birnin Kiev cewa, akwai alamar da ke nuna cewa, kasar Chaina na goyon bayan cikakken ikon yankin Kirikiya da Dombas ga Ukraine.

Karin bayani: Yunkurin sasanta rikicin Rasha da Ukraine

A halin yanzu dai Minista Kuleba na birnin Beijing, inda ya tabbatar da aniyar Kiev na tattaunawa da Moscow domin kawo karshen yakin da ake fama da shi. Ya zuwa yanzu dai, fadar mulki ta Kremlin ta mayar da zazzafan martani, inda ta ce Kasar Chaina na ci gaba da zama babbar kawar Rasha, don haka ake ganin cewar Chaina na tasiri sosai kan shawara da Rasha ke yankewa