1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na son a Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou
September 13, 2022

Jamus ta yi kira ga shugaba Vladimir Poutin da ya janye dakarun kasar daga Ukraine a cikin hanzari domin samun mafita a rikicin da ya barke tsakanin kasashen biyu

https://p.dw.com/p/4Gnka
Deutschland Bundeskanzler Olaf Scholz
Hoto: Annette Riedl/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a yayin tattaunawarsu ta waya da takwaransa na Rasha Vladimir Poutin ta tsawon mintoci 90, ya bukaci Rasha da ta dakatar da buda wuta, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya nuna cikakkiyar fata na ganin an samu masalaha ga rikicin Ukraine.

Gwamnatin Jamus ta kuma bukaci Rasha da ta cigaba da mutunta yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine da aka cimma karkashin jagorancin Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya.