1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kokarin ficewa da fararen daga Mariupol

Abdoulaye Mamane Amadou
March 31, 2022

Ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana shirinta na tsagaita bude wuta domin bada damar shigar da kayayakin agaji da kuma ficewa da fararen hula a yankin Mariupol na kasar Ukraine a wannan Alhamis.

https://p.dw.com/p/49GMj
Ukraine Krieg | Angriffe auf Mariupol
Hoto: Leon Klein/AA/picture alliance

A wata sanarwar da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar a ranar talata, ta ce matakin zai soma aiki ne a sanyin safiyar wannan Alhamis kana kuma Rasha za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin bayar da agaji na kasa da kasa irinsu Red Cros da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai tuni shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya nuna shakku kan sahihancin yunkurin na Rashar yana mai cewa a shirye dakarunsa suke su fafata da na Rasha a yankin Donbass da ke gabashin kasar.

Rahotanni sun ce Rasha ta yi luguden wuta kan birnin Tcherniguiv da Mariupol, inda rahotanni suka ce an kai wasu jerin hare-hare ciki har da kan wani bene na hukumar Red Cros, duk da yake magajin garin yankin bai yi wani karin haske a kai ba.

A nata bangare Michelle Bachelet, kwamishiniyar hukumar kare hakin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta zargi Rasha da aikata laifukan yaki a cikin wata doguwar makala da ta wallafa.