1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jiragen ruwan yaki na Rasha sun doshi zuwa Turai

March 17, 2022

Wannan na zuwa ne a yayin da tsohon ministan harkokin wajen Japan Taro Kono ya ce wajibi ne kasar ta sanya wa Rasha takunkumi idan tana son tsira da mutuncinta. 

https://p.dw.com/p/48bY5
Frankreich Kriegsschiff Mistral
Hoto: F.Perry/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Japan ta sanar da cewar ta hango manyan jiragen ruwa na yaki guda hudu mallakin kasar Rasha na ratsawa ta cikin gabar ruwanta, da alamu kuma, jiragen na dosawa ne zuwa nahiyar Turai. Irin wadannan jiragen ruwa dai kan dauki manyan tankokin yaki da sauran kayan yaki na sojoji kuma Japan ta ce ba ta saba ganin jiragen ruwan mallakin Rasha na wuce ta gabar tekunta ba.


Tsohon jami'in Japan Kono ya ce idan har kasar ba ta tallafa wa wadanda Rasha ta yi wa mamaya ba, to wata rana za a wayi gari China ta yi mata barazana kuma duniya nada zabin ta kawar da kai daga abin da China ka iya yi mata.