1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta bayyana rabuwar kai a NATO

Yusuf Bala Nayaya
April 3, 2019

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana a birnin na Washington cewa ba gudu ba ja da baya wajen siyan makami mai linzami daga Rasha.

https://p.dw.com/p/3GC81
Türkei Cavusoglu in Istanbul
Hoto: picture-alliance/AA/A. Hudaverdi Yaman

Turkiyya ta bayyana a wannan Laraba cewa za ta sayi makami mai linzami daga Rasha abin da ke nuna rabuwar kai tsakanin kasashen da ke taka rawa a kungiyar tsaro ta NATO daidai lokacin da kungiyar ke bude biki a birnin Washington na tunawa da shekaru 70 da kafuwar kungiyar.

Ministocin harkokin waje daga kasashen yamma 29 ana sa rai za su tsaya kai da fata wajen nuna turjiyarsu ga Rasha a yayin zaman da za su yi na kwanaki biyu a babban birnin na Amirka.

Ministan harkokin wajen Turkiyya dai Mevlut Cavusoglu ya bayyana a birnin na Washington cewa ba gudu ba ja da baya wajen siyan makamin mai linzami samfurin S-400 duk da barazanar da Amirka ke masu na dakatar da Turkiyya daga kawancen shirin jiragen nan da ake yaki da su ta sama da kasa samfurin F-35 fighter-jet.