Turkiyya ta soki Jamus da hana yin gangami
March 4, 2017Gwamnatocin biyu na Ankara da kuma Berlin na fama da tsamin dangantaka a yan kwanakin da suka wuce bayan da wasu garuruwan Jamus suka ki amincewa da taron da aka shiriya wani ministan Turkiyyar zai yi jawabi domin neman goyon bayan Turkawa mazauna jamus ga bukatar kuri'ar raba gardama da zaa gudanar a ranar 16 ga watan Aprilu da za ta bada damar gyaran kundin tsarin mulki domin baiwa shugaba Erdogan karin karfin iko.
Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce hukumomin jihohin da suka hana taron sun dauki matakin ne bisa tsarin doka kuma Jamus na martaba yancin al'uma na fadin albarkacin baki.
Ministan shari'a na Turkiyya Bekir Bozdag wanda aka shirya zai yi jawabi a taron ya zargi kasashen Turai da suka hana gudanar da tarukan da cewa su na adawa da gyaran kundin tsarin mulki ne saboda basa son Turkiyya ta zama mai karfin iko da kuma zaman lafiya.