1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya mayar wa da Amirka martani

Gazali Abdou Tasawa
August 4, 2018

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ba da umurnin rike kudaden ajiyar banki na ministan shari'a da kuma na cikin gida na kasar Amirka a kasarsa.

https://p.dw.com/p/32cgM
Türkische Präsident - Tayyip Erdogan
Hoto: Getty Images/AFP/B. Kilic

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ba da umurnin rike kudaden ajiyar banki na ministan shari'a da kuma na ministan cikin gida na kasar Amirka a kasarsa a matsayin martani ga wani mataki mai kama da irin wannan da Amirka ta dauka kan wasu ministocin Turkiyyar biyo bayan da mahukuntan Turkiyyar suka kama Andrew Brunson wani pasto dan asalin kasar Amirka mazauni Turkiyya da Ankara ke zargi da yi wa kungiyar Fetullah Güllen leken asiri. 

A wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin na kasa Shugaba Erdogan ya bayyana cewa sun nuna hakuri sosai amma hakurinsu a yanzu ya kawo karshe dan haka dole idan Amirka ta ce kul su ce mata cas. Shugaba Erdogan ya kara da cewa yin amfani da makamin tattalin arziki kan wama matsalar da ta siyasa ko ta shari'a ba zai zama alkhairi ga kasashen biyu ba.