1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta nemi kai wa al'umma dauki a Idlib

Yusuf Bala Nayaya
September 11, 2018

Wannan kira na zuwa ne yayin da dakarun Siriya da ke samun goyon bayan Rasha ke zafafa hare-hare kan yankin da ya yi saura inda 'yan tawaye suka ja daga.

https://p.dw.com/p/34fVw
Syrien Flüchtlinge Provinz Idlib
Hoto: Getty Images/AFP/A. Watad

Shugaban kasar Turkiyya  Recep Tayyip Erdogan a wannan Talata ya yi kira ga kasar Rasha da Iran su duba halin da al'ummar Siriya a yankin Idlib suke ciki kada a bari Shugaba Bashar al-Assad ya halaka su. Wannan kira na zuwa ne yayin da dakarun Siriya da ke samun goyon bayan Rasha ke zafafa hare-hare kan yankin da ya yi saura inda 'yan tawaye suka ja daga a kasar ta Siriya.

A wani labarin kuwa jakadan MDD kan rikicin na Siriya Staffan de Mistura na gana a wannan Talata da manyan jami'ai daga Rasha da Iran da Turkiyya a kokari na ganin an koma teburin tattaunawa da 'yan tawayen don kauce wa zubar da jini.