1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta kira taron gaggawa na ƙungiyar ƙawancen NATO

June 24, 2012

Domin ɗaukan matakan da suka dace dangane da jirgin saman yaƙinta da Siriya ta harbo Turkiyya ta kira taron ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO dan samun shawarar wakilan ƙungiyar

https://p.dw.com/p/15Kcj
Der tuerkische Staatspraesident Abdullah Guel, aufgenommen am Montag (19.09.11) im Schloss Bellevue in Berlin bei einer Pressekonferenz. Guel befindet sich auf einem viertaegigen Staatsbesuch in Deutschland. (zu dapd-Text) Foto: Nigel Treblin/dapd
Shugaban kasar Turkiyya Abdullah GülHoto: dapd

Masu binciken gano matuƙan jirgin saman yaƙin Turkiyyan da ya faɗi, sun gano wasu ƙarafan jirgin a cikin ruwayen Siriya da ke da zurfin mita dubu ɗaya da ɗari uku.

Gidan talabijin na ƙasa ya bayyana wannan cigaban da aka samu ba tare da ya fayyace majiyarsa ba. To sai dai har yanzu ba a kai ga gano matuƙan jirgin ba.

A halin da ke ciki dai wakilai daga ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO za su gudanar da wani taron gaggawa bayan da Turkiyya, wacce ke zama mamba a ƙungiyar ta nemi shawara dangane da irin matakan da ya kamata ta ɗauka.

Turkiyya ta gabatar da wannan buƙata ne bisa tanadin ƙuduri na huɗu, a yarjejeniyar da ta kafa wannan ƙungiyar tsaro.

Bisa tanadin wannan ƙudurin na huɗu, kowace mamba, na iya neman shawara a duk sadda take buƙata, idan har a ra'ayinsu an ɗauki wani mataki dake barazana ga tsaro, ko iyakokinsu ko kuma ma 'yancin siyasarsu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar