1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Turkiyya ta kame 'yan cirani 276

Binta Aliyu Zurmi MNA
July 7, 2020

'Yan sanda a Turkiyya sun yi nasarar damke mutane 276 'yan cirani a gabar tekun kasar da ke Aegean, da kuma wasu mutane 8 da ake shirin fidda su daga kasar. 

https://p.dw.com/p/3evBE
Europa Symbolbild Flüchtlingsboot auf dem Mittelmeer
Hoto: picture-alliance/Photoshot/M. Lolos

Tun a baya 'yan sanda suka fara ganin 'yan ciranin na yawan kai kawo a gabar tekun, hakan ya sa jami'an tsaro saka idanuwa musamman a yankin Izmir wanda ya kai su ga wannan nasarar.
Da yawa daga cikin 'yan ciranin da aka kama dai sun fito ne daga kasashen Siriya da Iran da Afganistan da kuma Somaliya.

A shekarar 2015 zuwa 2016 miliyoyin mutane ne suka isa kasar Girka daga Turkiyya, wanda a shekarar 2016 aka kulla yarjejeniya tsakanin Turkiyya da kungiyar tarayar Turai don kar kasar ta maida mutanen daga inda suka fito inda za a ba ta tukwici na kudi.