1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta kama 'yar uwar al-Baghdadi

November 5, 2019

Hukumomi a Turkiyya, sun cafke 'yar uwar tsohon jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi, wanda jami'an Amirka suka halaka a makon jiya a wani hari da Amirka ta kai arewacin Siriya.

https://p.dw.com/p/3STM2
Pentagon PK Veröffentlichung Bildmaterial al-Baghdadi Einsatz
Hoto: US Department of Defense

Gwamnatin Turkiyyar dai na zargin matar wato Rasmiya Awad, mai shekaru 65 da alaka da kungiyar IS a cewar wani jami'in dan sandan ciki.

Jami'an leken asirin Turkiyyar sun ce mataki ne na tattara bayanai kan kungiyar ta IS.

Kamen ya shafi matar ce da mijinta da surukarta da kuma wasu yara biyar, inda manya daga cikinsu ke amsa tambayoyi.

An kama su ne da yammacin ranar Litinin a garin Azaz da ke cikin lardin Aleppo na kasar Siriya.

Da ma dai yankin waje ne da Turkiyya ta sha kai wa farmaki musamman lokacin da take fatattakar mayakan kungiyar IS da kuma na Kurdawa a shekara ta 2016.