1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta cire dokar ta baci

Abdul-raheem Hassan
July 19, 2018

Gwamnatin Ankara ta janye dokar ta bacin shekaru biyu bayan da aka samu boren yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Erdowang a shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/31j9h
Bildergalerie Türkei Präsident Recep Tayyip Erdogan
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Bozoglu

Duk da cewa ana cike da fatan samun sukunin al'amura a Turkiyya bayan soke dokar ta bacin, amma 'yan adawa na fargabar  gwamnati ta sake tsawaita dokar mai tsanani, 'yan adawar na ganin a baya gwamnatin ta sha tsawaita dokar ta bacin har sau bakwai. Akalla mutane 80,000 aka rufe a gidajen kurkuku yayin da aka kori dubban ma'aikatan gwamnati cikin wa'adin dokar bisa zargin alaka da malamin addinin nan Fetullah Gulen  da ke samun mafaka a Amirka wanda gwamnatin Turkiyya ke zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura.