1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Turkiyya da na Rasha sun soma sintiri na hadin gwiwa

Abdoulaye Mamane Amadou
November 1, 2019

Sojojin Turkiyya da na Rasha sun fara sintirin hadin gwiwa a Siriya kamar yadda yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta ayyana wacce ta kawo karshen luguden wutar Turkiyya kan mayakan Kuradwa na YPG.

https://p.dw.com/p/3SLKw
Syrien Amuda russische Truppen patrouillieren im Norden
Hoto: AFP/D. Souleiman

Kafofin yada labaru sun tabbatar da hango sojojin kasashen biyu tun da sanyin safiyar Juma'a a kauyen Dirbassiyah da ke kusa da iyakar kasar Turkiyya da Siriya, kana kuma rundunar tsaro ta Turkiyya ta gayyaci manema labarai zuwa kaddamar da sintirin. 

Dama dai yarjejeniyar da Turkiyya da Rasha suka cimma ta tanadi ficewar dakarun mayakan Kuradawan na YPG daga yankin, ficewar da shugaban Turkiyyar Recep Tayyip Erdogan ya ce za a hakikance ne kawai idan sintirin da jami'an tsaron bangarorin biyu na Turkiya da Rasha suka kaddamar ya dore.