1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Turkiyya ta cafke wanda ta zarga da kai hari Cocin Santanbul

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 14, 2024

Maharan na da alaka da kungiyar ta'addanci ta ISKP da ta yi kaurin suna wajen hare-hare a Afghanistan

https://p.dw.com/p/4kcyo
Hoto: Ozan Kose/AFP

Hukumar leken asirin Turkiyya ta sanar da samun nasarar cafke wani 'dan kungiyar ta'addanci ta IS da ake kyautata zaton shi ne kanwa uwar gami wajen kulla tuggun kai hari mujami'ar Santa Maria Italian ta birnin Santanbul a farkon shekarar nan.

Karin bayani:Harin cocin Katolika na Istanbul ya yi sanadin mutuwa daya

Hukumar ta bayyana sunan mutumin da Vishan Soltamatov, wanda shi ake zargi da safarar makaman da aka kai harin da su a ranar 28 ga watan Janairun da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 'dan Turkiyya guda daya.

Karin bayani:Turkiyya ta lashi takobin hukunta masu hannu a harin Rafah

Maharan na da alaka da kungiyar ta'addanci ta ISKP da ta yi kaurin suna wajen hare-hare a Afghanistan, kuma a cikin watan Afirilun da ya gabata ma jamia'n tsaron Turkiyya sun kama mambobin kungiyar guda 48 da ke da hannu wajen kai farmakin na watan Janairu.