1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta amince da tsagaita wuta a Siriya

October 17, 2019

Shugaban Amirka Donald Trump ya yi marhabin da amince wa tsagaita buda wuta a arewacin Siriya, da shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya yi.

https://p.dw.com/p/3RTMh
Militärischer Konflikt in Nordsyrien | Türkischer Präsident Recep Tayyip Erdogan mit US-Vizepräsident Mike Pence
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Presidential Press Service

A wani sakon a shafinsa na Twitter, Shugaba Trump ya ce wannan labari na ceton rayukan miliyoyin mutane a yankin Kurdawa, abin farin ciki ne matuka.

A wata ganawar da ta wakana tsakanin mataimakin shugaban Amirka Mike Pence da shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan, Amirka da Turkiyya sun amince kan tsagaita buda wuta a arewacin Siriya.

Mr. Pence ya tabbatar da hakan ne 'yan mintuna bayan ganawar da suka yi a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.

A wannan Alhamis ne dai mataimakin shugaban na da ministan harkokin wajen kasar Mike Pompeo suka isa Turkiyya a kokarin kawo karshen hare-hare kan kan Kurdawan na Siriya.