1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Rashin kula ga masu HIV a Turkiyya

December 6, 2022

Har kawo yanzu batu kan cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA, batu ne da ba a tattaunawa ko ma yin magana a kansa a Turkiyya.

https://p.dw.com/p/4KYxV
Turkiyya | Önder Bora | HIV
Önder Bora na kungiyar bayar da gajai ta Pozitif-İzHoto: privat

Duk da cewa a hukumance yawan masu dauke da kwayar cutar a Turkiyyan bai kai yadda yake a wasu kasashe ba, sai dai kuma adadin masu dauke da HIV/AIDs ko kuma SIDA na karuwa ne maimakon ya ragu kamar yadda ake samu a wasu kasashen. Kungiyoyin bayar da agaji na kasar ta Turkiyya dai, na kokawa kan yadda suka ce ba a daukar korafinsu da muhimmanci. Koda yake wadanda ke da inshorar lafiya na hukuma na da damar samun kulawa a asibitoci, sai dai hakan zai yiwu ne kawai idan an gano mutum na dauke da kwayar cutar. Masu bayar da agajin dai, sun nunar da cewa sau tari hakan ba ta faruwa saboda wasu dalilai masu yawa musamman rashin wayar da kan al'umma. Kusan duk shekara ana samun rahoton wadanda suka kamu da cutar kimanin dubu biyu da 500 zuwa dubu uku a Turkiyya, baki daya dai akwai kimanin mutane dubu 32 da ke dauke da cutar mai karya garkuwar jiki a kasar.

Türkei Arda Karapınar
Arda Karapınar na kungiyar agaji ta Red Ribbon a TurkiyyaHoto: DW/T. Baykal

Za a iya cewa adadin bai taka kara ya karya ba, idan aka yi la'akari da al'ummar Turkiyyan da yawansu ya kai miliyan 85. Sai dai a hirarsa da DW, jami'in bayar da agaji Önder Bora na kungiyar agaji ta Pozitif-iz da ke taimakon masu dauke da cutar HIV/AIDs da kuma wayar da kan al'umma adadin abin damuwa ne ganin cewa mutane da dama ba su da masaniya kan cutar. Su kansu mahukuntan Ankaran dai sun tabbatar da karuwar adadin masu kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki, abin da Arda Karapinar na kungiyar bayar da agaji ta red ribbon a Turkiyyan ya bayyana da rahoto mara dadi daga Turkiyya. Ya kara da cewa wariya da kyamar da ake nunawa masu dauke da cutar ya sanya mutane da dama ba sa son a yi musu gwajin, kana koda an yi musu suna yin iya kokarinsu wajen ganin saun boye sakamakon ba tare da sun bayyana ba. Koda yake akwai wuraren yin gwaji a boye na kungiyoyin bayar da gajai, sai dai kuma a manyan biranen Turkiyyan kawai suke.