1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katin gargadi ga Shugaba Erdogan

Mohammad Nasiru Awal AS
April 1, 2019

Jam'iiyar AKP ta shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ta samu mummunan koma baya a zaben kananan hukumomi.

https://p.dw.com/p/3G1tZ
Türkei Ankara Kommunalwahlen CHP-Anhänger feiern
Hoto: Getty Images/AFP/A. Altan

A zaben kananan hukumomi da aka gudanar ranar Lahadi a kasar Turkiyya jam'iyyar AKP ta shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan ta samu babban koma baya. Sakamakon farko da aka bayar ya nuna cewa 'yan takarar jam'iyyar adawa ta CHP sun yi nasara a babban birnin kasar Ankara da kuma a birnin Santambul mai miliyoyin mazauna.

Asarar wadannan manyan biranen biyu dai na zame wa Shugaba Erdogan wani babban katin gargadi.

Zeynep Gurcanli da ke sharhi kan lamuran siyasar Turkiyya ta ce za a shiga sabon yanayi na siyasa a kasar.

"A karon farko Erdogan ba zai shugabanci kasar nan shi kadai ba. Dole ya nemi goyon bayan jam'iyyar 'yan kishin kasa. Wato ke nan wannan zai zama sabon kawance a tsarin siyasar Turkiya."

Jam'iyyar AKP dai ta ce idan zarafi ya kama za ta kalubalanci sakamakon zabe a kotu.