1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Turkiyya da Nijar sun kulla alakar makamashi da ma'adinai

July 18, 2024

Yayin ziyara da tawagar Turkiyya ta kai birnin Niamey, kasashen biyu sun amince da yarjeniyoyi muhimmai da suka shafi tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/4iTMN
Tawagar Turkiyya a Nijar
Tawagar Turkiyya a Nijar Hoto: PPRM Niger

Kasashen Turkiyya da Nijar sun amince su inganta alakarsu kan harkokin makamashi da hakar ma'adinai da kuma tsaro.Wannan na zuwa ne bayan kasar ta yammacin Afirka ta bukaci tsoffin abokan huldarta na kasashen yamma su fice daga cikinta. Nijar ta kuma haramta wa kasar Faransa wacce ta yi mata mulkin mallaka harkar ma'adinai.

Karin bayani:Nijar: 

Nijar ta kawo karshen huldar soji da Amurka

Tawagar Turkiyaa ta isa Niamey ranar Laraba kuma ta kunshi ministocin harkokin kasashen waje da na tsaro da makamashi da kuma  sauransu. Tawagar ta gana da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tiani kuma kasashen biyu sun amince kan yarjeniyoyi muhimmai da suka shafi tattalin arziki.

Karin bayani:Tiani ya juya wa yarjejeniyoyin tsaro da waje baya

Janar Tiani ya karbi mulki a watan Yulin shekara ta 2023 bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum Muhammed.