1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci ga masu boren Turkiyya na 2013

Ramatu Garba Baba
June 24, 2019

Daruruwan mutane sun yi dandanzo a harabar kotun da ke shirin yankewa wasu mutane 16 hukunci bisa zarginsu da aka yi da yunkurin juyin mulki a shekarar 2016. 

https://p.dw.com/p/3Kzpy
Veranstaltung  - „Freiheit für Osman Kavala“
Hoto: Maxim-Gorki-Theater

Osman Kavala fitaccen dan kasuwa kuma dan siyasa da wasu mutane15 da suka jagoranci zanga-zangar a wancan lokacin sun musunta zargin da ake musu, inda suka ce sun gudanar da zanga-zangar adawa da wasu tsare-tsare na kayata katafaren wurin shakatawa da ke birnin Santanbul da gwamnati ta shirya yi ne.

Tun a shekarar 2017 ake tsare da Kavala a wani gidan yarin kasar da ke wajen birnin Santanbul, kuma ya kalubalanci daurin da aka masa da ya ce an yi ne kan zargin da ba shi da tushe balle makama.

Gwamnatin Racep Tayyip Erdogan da ke zargin yi mata juyin mulkin, ta daura alhakin asarar rayuka da dukiya da aka samu kan wadanda suka jagoranci zanga-zangar shekaru shida da suka gabata da kuma suka fito daga jam'iyyun siyasa daban-daban. Idan har an same su da laifi, to za su fuskanci hukunci na daurin rai da rai.